Daga Nazifi Bala Dukawa
Hankalina ya karkata ga wani shafin Twitter na bogi wanda ke yaɗa labaran ƙarya da sunana. Ina so in sanarda duniya cewa banida Twitter account.
Yanzu-Yanzu: Ganduje ya kafa kwamitin mika mulki mai mutane 17
Bayanin hakan ya fito ta Hannun wata takarda da makusancin a kafafen yada labarai nazifi Bala dukawa ya sanyawa hannu, wanda ya aikowa kadaura24.
Ba zan biya duk wani bashi da Ganduje ya ciyo bayan zabe ba – Shawarar Abba Gida-gida ga bankuna
Banji daɗi ba sam bisa yanda wasu kafafen yaɗa labarai ke alaƙanta wancan account dani ba tare da sunyi bincike ba. Ina kira ga kafafen yaɗa labarai da su himmatu wajen bayar da rahotanni sahihai da kuma tantance majiyoyinsu kafin buga wani labari, musamman a wannan zamani da ake yada labaran ƙarya.
Ina kuma ƙara jaddada cewa a halin yanzu na mayar da hankali sosai wajen yin ayyukan alkhairi don cika alƙawuran yakin neman zaɓe da kuma samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar yankina.