Abba Gida-gida ya karrama yan kasuwar Singa yayin dawowarsa Kano bayan kammala aikin Hajji – Liti Kwasangwami

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar kwankwasiyya singa market dake jihar kano, ta yabawa Gwamnan kano injiniya Ababa Kabir yusuf bisa yadda ya nuna goyan bayansa ga kungiyar a lokacin daya dawo daga kasa mai tsarki a matsayinsa na Amirul hajji bayan kammala aikin hajjin bana.

Shugaban kungiyar Alh. Muntari Liti Kwasamgwami ne ya bayyana jim kadan bayan wucewar Gwamnan ta kasuwar singa domin nuna godiyarsa ga yan kwankwasiyya na kasuwar singa .

InShot 20250309 102512486
Talla

Alh. Liti kwasamkwami ya bayyana cewar, yan kungiyar kwankwasyya Singa market sun dade suna baiwa kwankwasiyya cikakkiyar gudunmawa ta fannoni da dama domin ganin Abba Kabir ya lashe zaben daya gabata,wanda kuma cikin ikon Allah aka samu nasara tun daga lokutan zabe har da yayin zuwa kotu, wanda daga bisani aka tabbatar Alhaji Abba Kabir a matsayin wanda ya ci zaben.

“Kungiyarmu sai da ta yi saukar karatun alkur’ani mai girma sau dubu daya domin ganin Gwamnatin jihar kano ta samu gagarumar nasara akan duk wani abu da ta sanya a gaba na hidimtawa al’ummar jihar kano wanda muke kyautata zaton Allah ya karbi Addu’ar domin yanzu duk titin da ka bi za ka ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na gudanar da ayyuka da fitar da magudanan ruwa domin kaucewa ambaliyar ruwa wannan ba karamar nasara ba ce ga alummar jihar”. Inji Kwasangwami

Kotu ta yanke wa Jarumin Kannywood, Kilina hukuncin shekara 1 a gidan yari

Shugaban ya ce ta fannin ilimi tun daga matakin furaimari zuwa sakandire da manya makarantu da jami’o’in na jihar kano an samu babbar nasara da za’a dade ana cin gajiyar irin wadannan ayyuka. Haka zalika, a bangaren tsaro da samar da zaman lafiya domin kare rayuka da dukiyoyin alummar jihar kano ba,a bar shi a baya ba .

Alh. Muntari Liti Kwasamgwami ya yi kira ga Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir yusuf, daya tuna da kungiyar kwankwasiyya singa market a rika sanya ta a cikin duk wasu abubuwa da suka taso a cikin ayyukan gwamnati domin ba da gudunmawa, musamman abin da ya shafi harkokin kasuwanci da abin daya taba yankasuwa,inda yace,yanzu haka ‘yan hamayya da suke kusa da su a cikin kasuwa dariya su ke yi musu wanda suke ganin kamar sun tura motane ta bulesu da hayaki.

Kwasangwami ya ce ya kamata Gwamnan kano Abba Kabir yusuf taimakawa wannan kungiya domin karfinta yana neman karewa saboda rashin tallafin daga gwamnatin wanda komai da karfi da jikinta take yi domin ganin gwamnatin kano ba ta durkushe ba akan aikace-aikacenta na yau da kullum.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Shugaban ya godewa gwamnan bisa yadda ya rika tiri-tiri da mahajjatan jihar kano musamman wadanda suka hadu da iftilin gobara a lokacin aikin hajji da yadda ya rabawa mahajjatan jihar kano riyal dari uku-uku domin tallafa musu.

Daga karshe ya bayyana cewar, kungiyar kwankwasiyya singa market ba za ta gajiya ba wajen bayyana ayyukan gwamnati a ciki da wajen kasuwar singa kamar yadda ta saba,inda kuma,ya bukaci alummar kasuwar singa da su ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar kano goyan bayan da suka kamata domin ganin ta samu damar aiwatar da ayyukan ci gaba ga alummar jihar kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...