Jarumar Nollywood, Mercy Aigbe, ta Musulunta

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman

 

Shahararriyar Jarumar Nollywood, Mercy Aigbe, ta musulunta.

 

Jarumar da mijinta, Kazeem Adeoti sun karbi bakuncin abokansu, da abokan aiki, da ’yan uwa yayain da suka shirya taron lacca na Ramadan, a karshen makon da ya gabata.

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya kafa kwamitin mika mulki mai mutane 17

 

Bayan nasarar taron an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da barin addinin Kiristanci zuwa addinin Musulunci.

 

 

A cikin wani faifan bidiyo da aka watsa, an gan ta tana bayyana sabon sunan musulunci da take so a rika kiranta da shi.

 

ZAƁAƁƁEN ƊAN MAJALISAR TARAYYA, ENGR. SAGIR KOKI, YA BARRANTA KANSA DA WANI SHAFI NA TWITTER

Ta bukaci ‘yan Najeriya da su rika kiranta da Hajiya Meenah Mercy Adeoti.

 

“Insha Allahu sabon sunana Hajia Meenah Mercy Adeoti, Ina matukar farin ciki sosai. Hakika wannan shi ne karatuna na farko na Ramadan sannan kuma Ramadan daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci. Kamar tara mutane ne mu sanar da su abin da Allah ya ce, domin mu bi ka’idojin da Allah ya tsara. Don haka na yi farin ciki da cewa mutanen da muka kira sun zo nan, ”in ji ta a cikin bidiyon.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...