Fiye da rabin yan Najeriya suna rayuwa cikin talauci – Gwamnatin tarayya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

 Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi 63 cikin 100 na mutanen Najeriya kusan miliyan 133 na fama da talauci.
 An gabatar da wannan adadi ne yayin da ake kaddamar da bincike kan Talauci na Najeriya Multidimensional Poverty Index (MPI) a Abuja ranar Alhamis.
 Majiyar Kadaura24 ta ruwaito cewa, ma’aunin da aka yi amfani da shi wajen kididdige wannan adadi ya samo asali ne a kan Multidimensional Poverty Index (MPI) Inda Akai la’akari da bangarori biyar wajen cikin wadanda suka hadar da kiwon lafiya, yadda ake rayuwa, da ilimi, da tsaro da kuma rashin aikin yi.
Talla
 Binciken wanda aka yi samfuri da gidaje sama da 56,000 a fadin Jihohi 36 na kasar nan da Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka gudanar tsakanin watan Nuwamba 2021 zuwa Fabrairu 2022, ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na talakawa, miliyan 86, suna zaune ne a Arewa, yayin da kashi 35, kusan kusan Miliyan 47 suna zaune a Kudu.
 Binciken ya bayyana jihar Sokoto a matsayin jihar da  tafi kowacce jiha yawan masu fama da talauci a fadin ƙasar,  inda take da kashi 91 cikin dari yayin da Ondo ke da kaso 27 cikin dari.
 Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an dauki matakin ne don gano adadin masu fama da talauci da kuma hanyoyin da Za’a fito da manufofi Masu kyau don kawar da talaucin a cikin al’umma.
 Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.
 Rahoton ya kara da cewa, “sama da rabin al’ummar Najeriya talakawa ne da suke amfani da kawayi ko ita ce wajen yin girki maimakon makamashi mai tsafta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...