Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar dake tallafawa masu fama da larurar cutar amosanin jini da wayar da kan al’umma muhimmancin yin gwaji kafin aure ta jihar kano, ta sha alwashin ci gaba da wayar da kan al’umma domin yin gwaji kafin a fadin jihar kano.
Shugaban kungiyar Alh muharazu Adamu Ibrahim Gizina ,Wanda mataimakinsa yakubu saidu ya wakilta ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai ziyarar wayar da kan matasa muhimmancin yin gwaji kafin aure, a makarantar sakandiren yan mata ta Bichi dake karamar hukumar Bichi .
Yakubu yace kasancwar cutar amosanin jini tana wahalar da kananan yara musamman a wannan lokaci na hunturu dake shigowa, shi yasa kungiyar ta kara kaimi da himma domin fadakar da al’umma musamman iyaye mahimmancin gwajin cututtuka da suka shafi yin ma’urata.

Yace gwajin cututtuka kafin a yi mu’amullar auratayya yana da mutukar mahimmanci musamman a wannan lokaci da cututtuka suka yi yawa ,Wanda akwai bukatar kulawa a kodayaushe domin kaucewa kamuwa daga cututtuka masu tarin yawa, wandanda a bayan ba’a san su ba.
A jawabinta shugabar makarantar sakandiren yan mata ta karamar hukumar Bichi, Hajiya Fatima Abubakar ta nuna farin cikinta bisa wananan ziyara da kungiyar ta kai makarantar sakandiren, domin wayar da kan al’umma da iyaye da ma yanmata amfanin yin gwaji kafin a yi aure.
Ta yi kira ga iyaye da masu hannu da shuni da uwa uba Gwamnatin wajen tallafawa yunkurin kungiyar na bata gudunmawar da ta kamata domin cimma nasarar da ta sanya a gaba.
Haka zalika, ta shawarci dalibai musamman yan mata da su kasance masu kulawa da kawunansu da tabbatar da nauin jininsu da kuma sana’ar da masu neman aurensu kan su je su yi gwaji kafin a yi nisa a cikin soyayyar juna, wadda ka iya kaiwa ga Aure.