Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers a ranar Larabar da ta gabata ya nemi afuwar tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, inda ya ce ya yi nadamar yin aiki domin sake zabar gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a watan Satumban 2020.
Wike ya baiwa Oshiomhole hakuri ne a wajen kaddamar da jirgin Rumuepirikom Flyover a karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar wanda Oshiomhole ya kaddamar.

“Yanzu mun zama abokai, mu manta duk abun da ya faru a baya,” Wike ya shaida wa Oshiomhole cikin murmushi.
A baya-bayan nan dai, Obaseki da Wike sun sami sabani hakan tasa suke yi takun-saka Saboda rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP a daidai lokacin da Obasake ke goyon bayan Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin da Wike ya ci gaba da neman Iyorchia Ayu da ya yi murabus a matsayin wani sharadi na goyon bayan takarar Atiku a zaben 2023.