Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana gamsuwar sa akan aikin da kasar Egypt zasu yi na samar da katafaran kamfani shinkafa wanda jihar Kano ce zata fi amfana da aikin a kasar nan.
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin shugabanin Gwamnatin Kasar Egypt dangane da aikin samar da wani kamfanin samar da shinkafa da zasu kafa a nan jihar Kano.
Mai Martaba Sarkin yace dangantakar dake tsakanin kasar masar da Nigeria musamman jihar Kano dangantaka ce dake kara habaka tattalin arzkin Kano da kasa baki daya.

Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa ya ce, masarautar kano za ta bayar da gudunmawar data dace wajen ganin an samar da cigaban tattalin arzkin Kano da Nigeria baki daya.
Mai Martaba Sarkin ya kuma yabawa kasar ta masar bisa gudummawar da suke bayarwa wajen ilimantar da al’ummar a kasar nan.
A nasa jawabi Shugaban kamafanin Egta Alhaji Bashir Yusif Ibrahim yace, jihar Kano zata ci gajiyar samar da kamfanin shinkafa mafi girma a kasar nan wanda kasar masar zata samar a jihar kano.
Haka zalika a wani cigaban kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin shugabanin hukumar zakka da Hubsi ta jiahr Kano karkashin jagorancin shugaban majalisar limaman juma’a Sheikh Muhammad Nasir limamin masallacin Sheikh Ahmadu Tijjani dake Kofar Mata a Kano.