Daga Nura Abubakar
Dan takarar wakilcin kura madobi da garin Mallam a jam’iyyar APC Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya sha alwashin da zarar yaje Majalisar wakilai ta kasa zai magance takaicin rashin wakilci na gari da al’ummar yankin suka dade suna fama da shi shekara da shekaru.
Musa Iliyasu Kwankwaso wanda yake shi ne Sarkin yaƙin Masarautar karaye yace ya tanadi kudirori wadanda zai Sanya a gaba da zarar yaje majalisa, Inda yace ya fahimci Rashin tanadin abun da za’a yiwa al’ummar yankin ne yasa suka tsinci kansu cikin halin da suke.
Kotu ta Fara Sauraron Shari’ar Muhd Abacha da Shugabannin PDP na mazabar sa
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Kadaura24 a ofishinsa, abubuwan da zai sanya a gaba idan mutanen kura madobi da garun Mallam sun zabe shi a matsayin wakilinsu a majalisar wakilai ta kasa .
” Akwai kudirori da Zamu je da su majalisar wadanda idan suka tabbata zamu inganta Rayuwar al’ummar da zamu wakilta musamman ta fuskar Noma wanda dama da shi muka shahara a wannan yakin namu”. Inji Musa Iliyasu
Yace kudirin sa na farko idan yaje majalisa shi ne zai gabatar da kudirin yadda za’a Kara inganta harkokin noma a yankin da Kuma tsarin yadda manoma zasu rage yawan asarar da suke yi idan sun noma, wanda hakan na karyar da gwiwar manoma .
“Nasan idan Allah ya taimaka kudirin ya wuce to babu shakka, za’a sami Karuwar arziki da kawaitar shi a cikin al’umma, Kuma hakan zai Kara tabbatar da yankin mu a matsayin cibiyar noma ta kasa da arewa baki daya”. A cewar Kwankwaso
Muna Cikin mawuyacin halin sakamakon lalacewar hanyar garinmu – Mutanen Garin Jar kuka
Yace ba wai yana nufin noma shinkafa kawai ba, a’a yana nufin ingata duk wani nau’in abu da ake shukawa ya fito a yankin tsakanin rani da damina.
Akwai cigaban tattaunawar tana nan tafe a nan gaba.