Yusuf Galambi dan majalisar wakilai ya sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Tajudeen Abbas, shugaban majalisar ne ya sanar da sauya shekar ta Galambi a wata wasika da aka karanta a zauren majalisar a yau Alhamis.
Ku ba mu hadin kai mu sauke nauyin da gwamnan Kano ya dora mana – Barr. Dan Almajiri ga mawadata
Dan majalisar shi ne ke wakiltar mazabar tarayya ta Gwaram a jihar Jigawa.

Galambi ya ce yanke shawarar komawa APC din sa ya samo asali ne daga βumarniβ daga mazabar sa.
Ya kuma danganta kudurinsa na barin jamβiyyar NNPP da rikicin shugabancin jamβiyyar.
Tuni dai dan majalisar ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje.