Na yi mamakin yadda na sami ma’aikatar Ilimi ta jihar kano – Hon. Abdullahi ‘Yan Shana

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Sabon kwamishinan ilimi na jihar Kano Rt. Hon. Ya’u Abdullahi ‘yan shana yace yayi matukar mamakin yadda ya Sami ma’aikatar Ilimi ta jihar kano Saboda tarin ma’aikatu da ma’aikatan da suka karkashin ma’aikatar.

Yace yaga mutane masu tarin yawa da yake da alaka da su ta hanyoyi daban-daban, musamman cikin Masu rike da shugabancin Hukumomin da ma’aikatun dake karkashin ma’aikatar Ilimi.
“Na yi aiyuka a matakai daban-daban a siyasance da Kuma aikin Majalisar da naje har kololuwa, sannan kuma a bangaren zartarwar na rike Mukamai daban-daban tun daga jiha har a gwamnatin tarayya, amma da nazu nan sai naga kamar bantaba aiki a ko’ina ba”. Inji sabon kwamishinan
 Yace bai yadda an yan uwa da abokan arziki sun raka shi ifis ba a ranar Litinin, saboda akwai kotu a kusa ma’aikatar Kuma hayaniyar jama’a zata iya damu kotu, yace hakan ce tasa a zabi ranar laraba domin a rakoshi, duk da haka sai da suka takaita yawan tawagar da suka raka shi.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a ranar laraba da yan uwa da abokan arziki suka raka shi ofis domin fara aiki.
 Wanda yace ga Amana ya bawa Abokan aikin nashi, Yana fatan suyi aiki tare su ciyar da ma’aikatar gaba bisa gaskiya da rikon Amana.
Yan shana ya yabawa ma’aikatan tare da yi musu alkawarin idan suka ba shi hadin kai zasu taimakawa yunkurin gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na inganta Ilimi a jihar kano.
Mai girma gwamna cikin Abubuwan Daya ke yi, ilimi na daga cikin abinda yasa a gaba, kasancewar shine gwamnan Daya kawo ilimi kyauta Kuma wajibi, inji Rt. Hon. Ya’u Yan Shana kwamishinan ilimn jihar Kano.
” Ma’aikatar ilimi tana daya daga cikin manyan ma’aikatu a jihar da ke da girma da fadi da Kuma Abubuwa masu yawa, don haka idan har kuka rike amanata kuma kuka bada cikkaken hadin kai babu shakka zanyi Nasara” a cewar kwamishinan.
“Duk Abinda kukazo dashi zamuyi shi bisa ka’ida da cancanta, Ina matukar godiya gareku don a kwanaki biyun da mukayi mun zauna da babbar sakatariyar wannan ma’aikata ta bamu shawarwari masu yawa, mun zauna da sauran wasu ma’aikatun naji inda aka tsaya, sannan naji inda ya kamata mu dora”. Inji ‘yan shana
Karshe ya ce dukkan daraktoci da shugabannin sassa na ma’aikatar da saura ma’aikata suma yana neman hadin kansu, domin burinsa bai wuce ace ma’aikatar ilimi ta samu cigaba da Kuma kykyawar Alaka tsakanin ma’aikatan baki daya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...