Kotu ta Fara Sauraron Shari’ar Muhd Abacha da Shugabannin PDP na mazabar sa

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Kotun majistiri dake zamanta a noman’s land karkashin mai shari’a Talatu Makama ta fara sauraron karar da yan sanda suka shigar suna karar wasu mutane guda biyu (2) Umar Alhassan da Auwalu Muhammad wadanda suke rike da shugabancin jam’iyyar PDP a mazabar Fagge B.

 

Kadaura24 ta rawaito tun da fari dai Muhammad Abacha ne ya rubutawa Babban Sufeton ‘yan-sandan Kasar nan koke, game da shugaban da sakataren jam’iyyar PDP na mazabar Fagge B, saboda sun ce shi ba dan jam’iyyar PDP ne saboda bai karbi katin jam’iyya ba kuma ba sunansa a rijistar PDP na mazabar ta Fagge B.

 

Kotun bayan ta saurari bangarorin biyu, lauyan mutanen biyu ya roki kotun data bada belin wadanda suke karewa. Inda dan sanda mai gabatar da kara Nura ya yi dogon suka kan bukatar bada belin, Bayan jin bangarorin biyu ne kuma mai shari’a Talatu Makama ta amince da rokon lauyan wadan da ake kara ta sa su a hannun belin a bisa sharuddai guda biyu.

 

Sharadi na farko shi ne kowannesu ya kawo mutum biyu (2) da zai tsaya masa, sannan sharadi na biyu kuma shine belin nasu na da ji lar kudi Naira Miliyan (1) daya kowannesu.

 

Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga wannan wata na Satumba da muke ciki domin cigaba da shari’ar.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa, Jafar Sani Bello ya yi karar Muhammad Abacha a gaban Babbar kotun tarayya dake zamanta a nan Kano, bisa zargin ya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP har ya yi nasara a zaben, ba kuma tare da ya ciki kaidojin jamiya kamar yadda suke kunshe a cikin tanade-tanaden kudin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ta shaida wa mazabar sa ta Fagge B aniyar sa takomowa jamiyar PDP tare da tabbatar da sunan sa ya shiga rijistar jamiyar a matakin mazabar tasa ta Fagge B.

 

Babbar kotun tarayyar dai zata fara sauraron shari’ar ne a ranar 14 ga wannan wata na Satumba cikin yarda Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...