Kotu a Kano ta bada umarnin Kamo Ado Gwanja, Safara’u da wasu yan Kannywood da TikTok

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

An maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi a Kano bisa zargin rashin tarbiyya.

Wasu majiyoyi sun ce laifuffukan sun haɗa da wakokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.

Sai dai Kadaura24 ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.

 

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano sun hada da 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Murja Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.

 

Murja Ibrahim

“Sakamakon karar da Muhd ​​Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd ​​Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.

“Alkali mai shari’a na Babbar Kotun Shari’a na Bichi a Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin a sama domin daukar matakin da ya dace.

“An maƙala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya,” in ji wasiƙar, wacce rijistaran kotun, Aminu Muhd ​​ya sanya wa hannu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Kamfanin NNPC ya rage farashin man fetur a Nigeria

Kamfanin albarkatun man fetur na Nigeria NNPCL ya rage...

Dawo da Gwadabe ya Jagoranci Anti Daba Hanya ce ta Magance Fadan Daba a Kano

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Rahotanni na tabbatar da cewa a...

APC a Kano ta magantu kan yunkurin Kwankwaso na shiga jam’iyyar

Shugaban jam'iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya yi...

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...