Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Date:

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar da ke cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, yana shirin komawa jam’iyyar APC.

Galadima, wanda na hannun damar Kwankwaso ne ya ce NNPP na bai wa ’yan Najeriya haske kan abin da jam’iyyar za ta iya bayarwa ta hanyar shugabanci nagari da na gaskiya, yana mai cewa ’yan siyasar da suka gaza ne kawai ke maganar zaben gaba tun kafin wa’adinsu ya kare.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A baya-bayan nan, Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai dawo APC, inda ya ce tsohon dan takarar shugaban kasa yana shirin sauya matsayi.

Sai dai a wata hira da The Guardian, Buba Galadima ya ce da ba don shugaba Bola Tinubu ba, da babu yadda za a ce wani irinsa da ya taba zama gwamnan Kano zai zama shugaban jam’iyyar kasa.

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Yayin da yake bayyana cewa ba wani mai hankali a Kano ko wani bangare na kasar da zai yi alfahari da dangantaka da APC a karkashin Ganduje, Galadima ya zargi shugaban jam’iyyar da kokarin amfani da NNPP don samun shahara a kafafen yada labarai.

InShot 20250309 102403344

Ya ce: “Na fara jin wannan daga gare ku. To, idan muka koma APC, shin za a ji daga bakin Ganduje ne? Ko don shi kadai ma babu wanda zai so komawa APC. Tinubu ne kadai zai iya sa Ganduje ya zama shugaban jam’iyya”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...