Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe gine-ginen da akayi ba bisa ka’ida ba a titin UDB dake kano.
Ana zargin rumfar shagon wata matashiyar ‘yar tiktok wato Rahama Sa’idu aikin ya rutsa da ita.

A safiyar Alhamis din nan matashiyar ta garzaya Hukumar Karbar Korafi ta Kano karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, inda ta zargi an cire mata allon sanarwa ba tare da an sanar mata ba, sai dai hukumar tace anbi ka’ida gabanin daukar hukuncin.
Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale
A yammacin wannan rana kuma hukumar ta KNUPDA ta kammala aikin rushe ragowar gurin da suka ce matashiyar ‘yar tiktok din tayi cin hanya.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a jiya ne hukumar KNUPDA ta cire allon tallan shagon jaruma Rahama Sa’ed , wanda hakan ya cecekuce a kafafen yada labaran.