An Kaddamar da littattafan warware matsalolin aure a kasar Hausa

Date:

Daga Rukayya Maida

Wata yar kishin kasa wadda take jagorantar wata kungiyar dake tallafawa marayu Aisha Aminu Ahli ta yi bikin Kaddamar da Wasu littafai guda 2 domin ba da tata gudunmawar wajen taimakawa rayuwa Ma’aura Musamman a kasar Hausa.

Kadaura24 ta rawaito a Zantawarta da Manema labarai bayan kammala taron Aisha Aminu Ahli tace ta rubuta littatafan ne Sakamakon yadda ta ga ana Samun Matsaloli da yawa a gidajen Ma’aurata Wanda hakan Kan haifar da mutuwar auren dungurumgum.

Da yake akwai Kungiyar da nake jagoranta don haka Ina Samun korafe-korafe Masu tarin yawa daga Ma’aurata wannna tasa na fahimci akwai buƙatar na bada tawa Gudunmawar wajen Magance Matsalolin” Inji Aisha Ahli

Hajiya Aisha tace littafi na Farko ta saka Masu Sunan “Mace-macen aure a Kasar Hausa wa ke da laifi ” wanda ya kunshi abubuwan da suke jawo Matsalolin aure da Kuma hanyoyin magance matsalolin.

Shi Kuma dayan sunansa ” Sirrin kwanciyar hankali mijinki a jakarki matar ka a aljihunka” shi kuma yana bayani ne akan rigakafin Matsalolin aure tun kafin a yi auren da Kuma bayan anyi auren.

“Ni Kadai na rubuta littatafan ba tare da wani ya tallafa min ba, sai dai na sami tallafin yan uwana da yan Kwamitin da mahaifina Allah yaji Kansa da Kuma Mijina” Inji Aisha Ahli

Aisha Aminu Ahli tace tuni an fara sayar da littatafan a Kasuwanni da Kuma Inda ake sayar da littatafai Musamman Ofishin gidan dabino dake mandawari gidan kankara.

Ta Kuma godewa dukkanin Waɗanda suka halacci taron Kaddamar da littatafan Musamman iyaye da Malamai a Jihar Kano dama Kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA

Daga Usman Usman   Ambassador Maryam Hassan shugabar kungiyar wayar da...

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...