Dangote Jagora ne wajen Samar da zaman lafiya a Najeriya – Ministan Tsaro

Date:

Daga Siyama Ibrahim
 Bisa yadda yake zuba jari mai yawa da kuma samar da ayyukan yi, an bayyana kamfanin Dangote a matsayin ginshiki wajen samar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Kadaura24 ta rawaito Ministan tsaro Bashir Salihi Magashi ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya ziyarci rumfar Dangote a wajen bikin baje kolin kasa da kasa karo na 43 na Kaduna.
 Ministan wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa Manjo Janar Ahmed Tijani Jibrin (Rtd) ya ce kamfanin ya yi tasiri sosai wajen inganta tsaro ta hanyar samar da ayyukan yi a kasar nan.
 Bayan gwamnatin tarayya Dangote ne na biyu wajen Samar da aikin yi a Nigeria.
 Dangote ne babban wanda ke daukar nauyin baje kolin kasuwanci na Kaduna da ake yi.
 Ya ce bincike ya nuna akwai alaka tsakanin yanayin tattalin arziki da tsaro, inda ya ce rukunin Kamfanonin Dangote ba wai samar da ayyukan yi kadai yake yi ba, har da tallafawa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
 Ministan ya yaba wa kamfanin bisa samar da kayayyakin da da ba’a samun su a Nigeria sai an shigo da su daga kasashen waje kuma cikin farashi Mai tsada,Amma ya ce yanzu yan Nigeria sun sami sauki.
 Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai da wanda suka shirya bikin baje kolin, kungiyar KADCCIMA, sun bayyana cewa sun samu kwarin gwuiwa da tallafin da Kamfanin Dangote ke bayarwa duk shekara domin bunkasa kasuwanci a Najeriya.
 Da yake jawabi a wajen bikin bude taron, Darakta Janar na KADCCIMA Usman Saulawa ya yaba da alakar da ke tsakanin rukunin Dangote da cibiyar.
 “Rukunin Dangote alama ce ta duniya a duniyar kasuwanci da masana’antu.  Hakanan zan iya ƙarawa da cewa wajibi ne a kowane gida sai an sami kayan Kamfanin Dangote ko kuma wani ya amfana da ayyukan jin kai ta gidauniyar Dangote ke gudanarwa,” inji shi.
 Ya ce kamfanoni daga Indiya, Pakistan, Morocco, Chadi, Senegal, Mali, Jamhuriyar Nijar da kuma Bangladesh sun halarci bikin baje kolin na bana.
 Kamfanonin da ke halartar taron a karkashin masana’antun Dangote sun hada da Dangote Cement, Dangote Sugar, NASCON, da Takin Dangote .
 Sanarwar da Sashen yada labarai na Kamfanin Dangote ya fitar ta ce mahalarta taron da ke neman yin kasuwanci da duk wani reshen kamfanin na iya cin gajiyar irin wannan damar a rumfar Kamfanin.
 Ta bayyana jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin manyan kasuwanninta a kasar nan, idan aka yi la’akari da matsayinta na tarihi a matsayin hedkwatar siyasar Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...