Daga Khadija Abdullahi Adam
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar wakilai kuma Dan Majalisar Mai wakiltar Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon Alhassan Ado Doguwa ya aike da Sakon ta’aziyyar Sarkin Ban Kano Alhaji Mukhtar Adnan .
Cikin Wata Sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Majalisar wakilai Auwal Ali Sufi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Sanarwa tace Sarkin Ban Kano uba ne a Jihar Kano da Nigeria baki Wanda ya bayar da gagarumar Gudunmawa wajen taimakawa al’umma ta fuskoki da dama.
Doguwa yace Yana Mika ta’aziyyar sa ga Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi da al’ummar Ƙaramar Hukumar Danbatta da al’ummar Jihar Kano baki daya .
Ya Kuma Yi Masa fatan samun rahamar Ubangiji subhanahu wata’ala tare da fatan iyalansa al’ummar sa zasu jure rashinsa .
קמגרה למכירה במודיעין פעמים רבות אנחנו יודעים שאנחנו צריכים לעשות משהו, אבל “רק הפעם” פשוט נמנעים מלעשות את זה, פשוט כי זה דורש יותר מדי מאמץ. אותו הדבר ������� ������� ��� �������