Shekarau ya bayyana yadda sukai da Bola Tinubu

Date:

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau sun gana a karon farko tun bayan rikici ya barke a jam’iyyar tasu reshen jihar Kano.

Rikicin , wanda ya sa Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano ballewa daga bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka kira kansu G-7, ya kuma sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na jiha.

A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wadannan zabuka sun raba kawunan ‘yan jam’iyyar ta APC a a jiar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya. Hasalima rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau suna yi wa juna shagube.

Sanata Shekarau ya shaida wa BBC Hausa cewa rashin iya jagorancin jam’iyya daga Gwamna Ganduje ne silar rikicin da jam’iyyar APC ke fama da shi a jihar.

Sai dai hukuncin da wata babbar kotu a Abuja ta yi a makon jiya ya ayyana bangaren Sanata Shekarau a matsayin halastaccen bangare a zaben shugabannin jam’iyyar.

Amma wannan hukunci bai yi wa bangaren Gwamna Ganduje dadi ba inda ya sha alwashin kalubalantarsa a kotu ta gaba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...