Masu Gadin Wata Mayanka sun yi karar Sarkin Fawar Kano a Kotu

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida
6, ga Disamba 2021
Kotun Majistry Mai lamba 21 dake zaune a Miller Road a Kano karkashin Jagorancin Mai Shari’a Abdu Mai Wada Abubakar ta fara saurar karar da wani Mai Suna  Ibrahim Iro da  Masu gadin Dabbobi suka yi karar Sarkin Fawar Kano Alh Isyaku Alin Muli, kan Zargin ya karbe musu ikon Dibar Taki Wanda Suke Tarawa sama da Shekara 50.
Masu karar Wanda suka bayyana cewa Tun asalin Kafa mayankar Abbatuwan, masu gadi ne Suke Dibar takin a matsayin Ladan aikin su na kula da Dabbobi a mayankar.
Lauyan masu Kara Barr. Baffa Umar Adam ya bayyanawa Alkalin kotun cewa duk sarakunan Fawar da akayi a Kano basa cewa Takin nasu ne, sai shi Sarkin Fawar na Yanzu.
Anan ne lauyan masu kara Barr. Salisu Sale ya bayyanawa kotun cewa masu Kara basu kawo musu takardar kiran kotu akan lokaci ba, a Don haka Suna bukatar kotun ta sanya wata ranar domin bayyana matsayar su akan Zargin da akewa Sarkin Fawar Kano Alh Isyaku Alin Muli.
Daga nan Mai Shari,ar Abdu Mai wada Abubakar ya dage saurar karar Zuwa ranar 25 ga watan January sabuwar Shekara ta 2022.

23 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...

NUJ@70: Gwamnan Kano ya karbi lambar girmamawa daga yan jarida

Daga Rukayya Abdullahi Maida Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Nigeria (NUJ)...