Sheikh Gumi ya Gina Makaranta a Daji don Makiyaya a Kaduna

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Ahmad Gumi, ya gina makarantar makiyaya a Kagarko da ke kusa da dajin kauyen Kohoto a matsayin hanyar magance matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna.
 Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, malamin ya sanyawa makarantar sunan cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio.
 Gidauniyar Sultan Mosque Foundation Limited ce ta dauki nauyin gudanar da aikin don Ilimantar da makiyayan Saboda su guji Shiga harkokin ta’addanci.
 “Idan sun yi ilimi, ba za su yi abin da suke yi ba” inji Gumi
 “Saboda haka, muka ce Bari mu Fara Samar musu da ilimi tun daga tushe, kuma mun fara aikin don ya zama abin koyi ga kananan hukumomi, jihohi da tarayya da kuma masu hannu da shuni da  kungiyoyin hadin gwiwa da su Zo mu hada Kai mu tabbatar an Ilimantar da makiyayan don duk abin da suke Rashin ilimi ne yake haddasa su.
Kadaura24 ta rawaito da ma dai Shehun Malamin ya Dade Yana fadin Rashin ilimi ne yake haddasa ta’addancin da makiyayan keyi, Kuma ya bada tabbacin idan Suka Sami Ilimi za su dai na abubuwan da suke.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...