Lawan Ahmad ya bayyana Dalilinsa na hada Wasan Hausa da Siyasa

Date:

Daga Umar Hassan
Shahararren Jarumin Kannywood kuma Furodusan fun din Izzar So, Ahmad Lawan ya bayyana dalilan da suka sa ya zabi hada  wasan Hausa da kuma siyasa.
 Jarumin haifaffen Jihar Katsina ya bayyana cewa ya shiga siyasa ne saboda sana’arsa ta nishadantarwa tana da hulda da jama’a kai tsaye.
 Lawan Ahmad ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Daily News 24 a Kano.
 Ahmad ya ce: “Na shiga siyasa ne saboda muna hulda da jama’a.  Kuma kamar yadda muke yi, wasu suna zuwa wurinmu don neman taimako. Don haka, na ji tunda ba na cikin gwamnati, dole ne in shiga siyasa don in sami damar tallafawa mutane da yawa a lokacin da suke buƙata ta.”
 Jarumin na Kannywood ya kara da cewa “Ina siyasa ko Allah zai ba ni damar mulkin jama’a. Zan yi farin ciki saboda in tallafawa mutane. “
 Furodusan Fim din na Izzar So ya dage da cewa ba shi da lokacin barin siyasa.
 “Ni dan siyasa ne kuma zan kasance a Cikin ta koyaushe.  Na san idan lokacin zabe ya zo, ko da ban tsaya takara ba, abokaina za su yi.  Kuma, dukkanmu za mu yi aiki don cimma manufar. “
 Lawan Ahmad  yana da shekaru 39 a duniya. An haife shi a jihar Katsina. Jarumi ne Kuma Darakta sannnan Mai shirya Fina-Finai a masana’antar Kanywood,  Lawan ya yi aure Kuma yana da ’ya’ya biyu.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...