Daga Zainab Muhd Darmanawa
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa tana Amfani da na’urorin fasahar zamani irin su CCTV domin magance matsalolin rashin tsaro da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din nan lokacin da ya karbi bakuncin babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya dake Kaduna, Manjo Janar Kabiru Imam Muktar wanda ya kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano.
Cikin Wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa Fagge ya aikowa Kadaura24 tace Dr. Gawuna ya ce, sanya na’urorin zamani ya taimaka matuka wajen dakile ayyukan ta’addanci da a baya suka yiwa jihar katutu.
Ya bayyana cewa, Kano a yau tana daya daga cikin jihohin kasar nan mafi zaman lafiya saboda addu’o’i da hadin kai tsakanin gwamnati da dukkanin hukumomin tsaro.
“A Kano muna gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin nazarin ayyukanmu da kuma tsara hanyoyin da za mu bi, hasali ma mun sanya dukkanin Masu damara cikin majalisar tsaro ta jiha.
Daga nan sai ya ba da tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga rundunar sojojin Nijeriya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’ummar Kano.
Da yake jawabi, babban kwamandan runduna ta daya, ta rundunar sojojin Najeriya dake Kaduna, Manjo Janar Kabiru Imam Muktar ya ce ya ziyarci rundunar sojin da ke karkashinsa a jihar Kano.
Ya bayyana cewa ingantattun bayanan da suke samu daga al’ummar Kano su na taimaka musu matuka wajen yakar Masu aikata miyagun laifuka.
“Haɗin kai da goyon bayan da mutanen Kano suka ba mu ya taimaka sosai a ƙoƙarinmu na shawo kan aikata laifuka komi ƙanƙanta a kano”.
“Muna godiya ga sarakunan gargajiya da al’umma bisa rawar da suke takawa wajen dakile rikicin manoma da makiyaya a jihar”.“Hakika na yi farin ciki da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jami’an mu na soji da mutanen Kano.” Inji shi.
Manjo Janar Muktar yayin da yake nanata kudurinsu na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano, ya yabawa Gwamnan bisa gudanar da ayyuka da ake yabawa a Jihar.
קמגרה תשדרג לכם את חיי המין ותאפשר לכם הנאה מרבית מהאקט. לטבע פלז’ר שלל פתרונות טבעיים נוספים שישדרגו לכם את חדר המיטות. מכוני ליווי