Daga Nura Abubakar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci matasan Najeriya da su ci gaba da jajircewa kada su gajiya wajen cimma manufofinsu.
Ya kuma bukace su da kada su gaji wajen fuskantar kalubale, inda ya ba su tabbacin za su kai ga Samun nasara.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne jawabi lokacin da yake bude taron matasa na kasa na kwanaki uku a babban filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.
Da yake Kara musu gwarin gwiwa la’akari da gagarumin damar, kirkire-kirkire da sana’o’in matasan Najeriya, Shugaba Buhari ya ce sana’o’in nishadi da kade-kade, wasanni, fasaha da sauran fannoni Sune Waɗanda matasa Suka fi Maida hankali akan su ,yace zasu taimaka sosai Wajen bunkasa tattalin arzikin su da Kuma basu damar cimma burikansu.