Zargin Bata Sunan Ganduje : Kotu ta ba da Umarnin tsare Muazu Magaji

Date:

Daga Zubaida Abubakar Ahmad
Kotun Majistare a  jihar Kano karkashin jagorancin Aminu Gabari ta bayar da umarnin tsare wani Muazu Magaji a gidan yari bisa zarginsa da bata sunan gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ‘ya’yansa Abdul,ziz Ganduje da kuma Balaraba Ganduje.
 A cewar rahoton farko (FIR) an gurfanar da mutanen biyu a gaban kuliya bisa zargin hada baki, cin zarafi, tayar da hankulan jama’a da bata sunan mutum wanda ya sabawa sashi na 97, 114, 391 da 399 na kundin laifuffuka.
 “A ranar 26 ga Oktoba, 2021 da misalin karfe 1100 na safiyar yau ne Honourable Auwal Lawal Shuaibu, shugaban karamar hukumar Nassarawa ya zo ofishin yan Sanda (SIB) Kano inda ya kai karar su Mu’azu Magaji Danbala da Jamilu Shehu Waɗanda dukkanin su yan Karamar Hukumar Kiru ne a Jihar Kano.
 “ A ranar 26 ga Oktoba, 2021 da misalin karfe 1100 na safe ku ka  hada baki kuka yada hoton mai girma gwamnan jihar Kano da ‘ya’yansa Abdul’aziz Ganduje da Balaraba Ganduje a Dandalin Facebook tare da rubuta mummunan kalma akan su ta ‘Barayin Kano”.  ‘ da sanin cewa matakin da kuka dauka zai iya haifar da rashin zaman lafiya a cikin jihar da kuma wajenta.
 “Don haka ana zargin ku da aikata laifukan da aka ambata a sama”.
 Wadanda ake zargin dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, inda daga nan ne lauya Mai kariya ya nemi a bayar da belinsa.
 Kotun dai ta ki amincewa ta bayar da belin wanda ake zargin bayan da lauyan masu kara Barista Wada Ahmad Wada babban Lauyan jihar ya soki hakan.
 Jaridar Justice watch ta rawaito Alkalin kotun, ya umurci sashin Binciken manyan Laifuka na Rundunar ‘yan sandan wato (SCID) da ta gabatar da takardar domin kotu ta duba yiwuwar za ta ba shi beli ko a’a.
 An dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga Nuwamba, 2021 don ci gaba da shari’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...