Daga Nura Abubakar Bichi
Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da Cewa uwar jam’iyyar APC ta Kasa ta Amince da Shugabanci Abdullahi Abbas a Matsayin halastacce Shugaban jam’iyyar APC na Jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya bayyana hakan ne Yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Wanda ake yi mako-mako a Gidan gwamnati.
Ganduje yace bayan Mika Rahoto da Sakamakon zaben da aka yi na Shugabanin jam’iyyar APC a kano , jam’iyyar tace batasan kowa a Matsayin Shugaban APCn ba sai Abdullahi Abbas da Sauran Shugabanin da aka zaba.
” Uwar Jam’iyyar APC ta tabbatar Mana da Amince da Shugabanin da muka zaba, ta Kuma ce bata san kowa a Matsayin Shugaban ba sai Waɗanda Muka zaba ” inji Ganduje
Gwamna Ganduje ya Kuma bayyana Cewa yanu suna ta kokarin ganin an sasanta da bangaren su Malam Ibrahim Shekarau, Inda yace dama haka Siyasa ta gada a bata Kuma a zo a Shirya.
Idan ba’a mantaba Kadaura24 ta rawaito Cewa an Sami Rashin jituwa tsakanin bangaren Gwamnati da Kuma bangaren su Malam Ibrahim Shekarau Waɗanda Suke ganin ba’a damawa da su a sha’anin da ya Shafi Shugabancin jam’iyyar APC a kano.