Har yanzu jam’iyyar APC ta kasa bata tabbatar da waye shugaban ta ba a Kano – Isma’il Ahmad

Date:

 

Guda daga cikin ‘yan kwamatin riko na uwar jam’iyyar APC ta kasa, kuma shugaban matasa na kasa Isma’il Ahmad ya bayyana cewar har yanzu uwar jam’iyyar APC ta kasa bata kai ga ayyana waye sahihin shugaban jam’iyyar a Kano ba.

 

Isma’il Ahmad ya bayyana hakan ne a Wata Zantawa da sukai da  gidan Rediyo Freedom dake Kano, inda yace uwar jam’iyyar zata yi nazari sannan ta fadi matsayarta akan shugabancin jam’iyyar reshen jihar Kano.

 

A karshen makon jiya ne dai aka samu bangarori guda biyu masu hamayya da juna na ikirarin sune halastattun shugabannin jam’iyyar bayan da kowanne yake ikirarin an zabe shi tsakanin bangaren Abdullahi Abbas dake tare da Gwamnatin Kano, da kuma bangaren Danzago da suke tare da Sanata Ibrahim Shekarau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...