Daga Nusiba Rabi’u Yusuf
Hukumomi a Kasar Mai tsarki sun bayyana cewa bayan Samun nasarar da ake a yaki da Annubar Covid-19, yanzu haka za’a sassauta Matakai Masu tsari da aka dauka a Masallatan Haramin Makka da Madina.
Ma’aikatar Cikin gida ta Kasar Saudia ita ce ta bada Sanarwar hakan Kamar yadda Kamfanin dillacin labarai na Routers ya rawaito.
Sanarwar tace gwamnatin za ta dage matakan bada tazara kuma za ta ba da damar Cika a Masallatan Harami biyu na Makka da Madina ga wadanda suka karbi cikakkiyar allurar rigakafi Corona.
Hukumomin sun ce an soke duk Wata dokar Corona data hana mutane haduwa a wuraren taro, motocin haya,gidajen abinci da sinima.
Haka Kuma sun ce Sanya takunkumin fuska bai zama tilas ba a wuraren taruwar jama’a Amma fa ga Waɗanda Suka yi Allurar rigakafin Corona Kashi na 1 da na 2.