Tsagin APC da ke adawa da salon shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano bai samu damar gudanar da zaɓen shugabancin jam’iyyar ba yayin da ɓangaren gwamnati ke aiwatar da nasa.
Ɓangaren wanda tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da wasu ‘yan majalisar tarayya ke jagoranta ya shirya gudanar da zaɓen ne a Sani Abacha Youth Center.
Sai dai ‘yan sanda sun hana kowa shiga wurin taron, kamar yadda wakilin BBC a Kano Khalifa Dokaji ya bayyana.
Jagororin taron sun bayyana cewa za su sanar da wata ranar da za su gudanar da zaɓen.
Wani bidiyo da aka wallafa a Facebook ya nuna yadda mutane suka yi cincirundo a ƙofar shiga wurin.
A gefe guda kuma, ɓangaren Gwamna Umar Ganduje na gudanar da zaɓen a rufaffen filin wasa na Sani Abacha, kuma gwamnan ya ce su ne kaɗai shugabancin jam’iyyar na ƙasa ya amince su yi zaɓen a yau Asabar.
Ya ƙara da cewa za su nemi ɗaya ɓangaren domin tattaunawa.
Allah ya kyauta