Daga Ibrahim Sani Gama
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata 19 ga Oktoba, 2021 a matsayin Ranar Hutu don murnar bikin Maulidin na wannan shekarar don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (Sallal-lahu alaihi wa sallam).
Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya yi wannan sanarwar a madadin Gwamnatin Tarayya, yana ya taya dukkan musulmin da ke cikin gida Nigeria da na kasashen waje murnar bikin wannan shekarar.
Ya shawarci dukkan ‘yan Najeriya da su sanya soyayya, hakuri da juriya a rayuwar su Kamar yadda wadanda su ne dabi’un Annabi Muhammadu (saw), Inda ya kara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Ogbeni Aregbesola ya umarci ‘yan Najeriya, musamman Musulmai, da su guji tashin hankali, rashin bin doka da sauran ayyukan da basu kamata ba.
Minista yayi kira da a dakatar da duk wasu abubuwan da ke kawo rarrabuwar kawuna a fadin kasar, ya Kuma bukaci dukkan ‘yan Najeriya musamman matasa, da su rungumi dabi’un na gari Inda yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na kokarin gina kasa don cigaban al’ummar Nigeria.