Rashin kyakykyawan albashi, Musgunawa sun sa wani Ma’aikacin Nas Radio Yola ya ajiye Aikinsa

Date:

Gidan radion NAS Fm Yola ta dauko hanyar rasa ma’akatanta saboda rage albashi da kuma rikon sakainar kashin da takeyiwa ma’aikatanta.

A takardar ajiye aikin da ya aikawa Hukumar gudanarwar gidan radio, daya daga cikin ma’aikacin gidan redion Zaiyad Ismail wanda shine yake gabatar da shirin #Ina_Matasa yace ya ajiye aiki ne saboda rashin adalcin da akeyi, kana yace a ranar Asabar da ta gabata ya gayyaci Dan Majalisan Jaha mai wakiltar Karamar Hukumar Gombi Hon. Japhet Kefas domin gabatar da shiri akan samun ‘yancin Najeria, suna cikin gabatar da shirin kwatsam shugaban kafar yace ya dakatar da shirin, a saka wani shiri daban.

Zaiyad yace ya kira shugaban kafar ta a waya akan dalilin da yasa akace ya dakatar da shirin alhali awa daya ne aka debawa shirin kuma minti talatin kawai yayi? Shugaban kafar yace ai an rage lokacin shirin ne, ba irin rokon da baiyi masa ba akan ya barshi ya karasa shirin tunda ya gayyaci babban bako, amma shugaban yaki.

Ya kara da cewa hukumar gudanarwa ta Nas Fm karkashin jagorancin Musa Waziri Hardawa yana nuna banbanci tsakanin ma’aikata, inda zakaga mai kwalin Difloma yafi mai Degree albashi.

Zaiyad Ismail yace akwai abubuwa da dama da ake aikatawa a wannan gidan radion wanda ya sabawa ka’ida, kuma wanda ya assasa gidan radion baida labarin duk abubuwan da yake faruwa.

Majiyarmu tayi kokarin Jin ta bakin Shugaban Gidan Radio Amma wayarsa taba shiga har Lokacin hada Wannan rahotannon.

13 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...