2021 Ranar Malamai : Matsalar Rashin Karin girma ce Babbar Matsalar mu a Kano

Date:

Daga Halima M Abubakar

Shugaban Kungiyar Malaman makarantu ta Kasa reshen jihar Kano com. Muhd Hambali Kura ya bayyana cewa Babbar Matsalar da malaman makaranta suke fuskanta a jihar Kano bai wuce Rashin Karin girma ba.

Com. Muhd Hambali ya bayyana hakan ne Yayin da yake ganawa da Jaridar Kadaura24 a Wani bangare na bikin Ranar Malamai ta duniya ta Shekara ta 2021.

Com. Hambali yace a shekarun baya gwamnatin Kano ta rage Wannan matsala ,Amma Yanzu ta sake dawowa domin akwai Malamai Masu tarin yawa da suke bukatar Karin girman bayan kuma lokacin yi musu Karin yayi wasuma ya wuce.

Ya bukaci Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Daya duba koken nasu ya Magance musu Matsalar,Inda yace Magance Matsalar zata taimakawa Malaman su Sami karkashin baiwa dalibai Ilimi Mai inganci.

Da yake taya Malaman Murnar zagayowar Wannan Rana Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Malaman bisa Gudunmawar da suke bayarwa don cigaban ilima a Kano.

Gwamnan ya bayyana irin kokarin da Gwamnatin Kano keyi na inganta harkokin Ilimi,Sannan ya baiwa Malaman tabbacin za’a ciyar da wadanda suka chanchanta gaba nan bada dadewa ba.

Majalisar Dinkin duniya ce dai ta ware ranar 5 ga watan disamba na kowacce shekara ta zamo Ranar Malaman makarantu ta Duniya, domin yin duba kan Matsaloli da nasarorin da malaman makarantu suke fuskanta a Duniya don Magance Matsalolin.

12 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...