Rashin Hanya yasa al’ummar Wani Gari kin Yarda a yiwa ‘ya’yansu Allurar Polio

Date:

Daga Rabi’u Usman

Wasu Mutane daga Cikin Al’ummar yankin Garin Unguwar Duniya dake Cikin Karamar Hukumar Dawakin Kudu Sunki Amincewa ayi wa yaran Su Allurar Riga Kafin Cutar Shan Inna Wadda ake Kira da Polio a takaice.

Inda Suka ce Sunfi Bukatar ayi musu aikin Hanya da Kuma Dakatar da Zaizayar kasar da ta Soma Cinye Musu Gidaje da Gonaki a Sakamakon Allurar Polio.

Suna Mai Cewar, Sun Mika Koken Su ga Mahukunta Akan Su Kawo Musu Dauki na Gaggawa Kafin a fara Rasa Rayuka a Cikin Wannan Gari Amma Abin yace tura Kamar yanda Al’ummar ke Shaidawa Wakilin Kadaura24.

Saidai Sakataren Kungiyar Cigaban Matasan garin Unguwar Duniya (Unguwar Duniya youth Development) Auwal Abdulmumini ya Shaida Mana Cewar, Lallai Sun yarda da Riga Kafin, Amma Babbar Bukatar su Shi ne Wannan Hanyar nan, Amma har yanzu Babu Wani Mai rke da Madafun iko da ya Waiwayi Hanyar,Shi isa Suka ce “Zamu Mika Sakon Mu inda Baza Mu iya zuwa ba”

A Nasa Bangaren Dagacin Garin Unguwar Duniya Alhaji Yunusa Lawan ya Bayyana Cewar, Shi da Masu Unguwannin Suna kan Wayar da Kan Mutanen Garin Akan Gudanar da Allurar Riga Kafin Cutar Shan Inna a Garin.

A Karshe dai Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Dawakin Kudu Abba Muhammad Inuwa ya Hakur kurtar da Jama’ar garin, Sannan ya Alkawarta Musu Cewar, Karamar Hukumar Nayin Kokarin ganin anyi Musu Wani Abu Mai Muhimmanci akan Matsalar Wannan Hanyar.

A Karshe dai har Wakilin mu ya Baro garin har zuwa Karfe 2pm Ba’a Samu an yiwa Mutanen Garin Polio ba.

Abin jira a gani a Nan Shi ne, Ko Mahukunta Za Suyi Kokari Akan Wannan Gagarumar Matsala a garin Unguwar Duniya?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...

Yadda Shugabanni da jagororin Jam’iyyar APC na Kano suka kauracewa tarbar Kashim Shattima yayi ziyarar ta’aziyya

Daga Fatima Mahmoud Diso   Shugabanni da jagororin jam'iyyar APC na...