Daga Munnira Sani sheshe
Tsohon Shugaban Kasar Nan Zamanin Soji Ibrahim Badamasi Babaginda yace ya fi Shugaba Muhammadu Buhari yaki da cin hanci da rashawa.
Tsohon shugaban kasar ya fadi haka ne a wata hira da aka yi dashi a Gidan Talabijin na ARISE TV a ranar Juma’ar nan.
Ya ce mutanen da ke karkashin sa waliyyai ne idan aka kwatanta da wadanda ke kan mulki a yanzu.
IBB ya ce a Lokacinsa ya tuhumi Wani tsohon gwamnan mulkin soja kan karkatar da dubban daruruwan mutane wadanda suka karkatar da biliyoyin kudi suna, Amma Yanzu Masu cin hanci tafiya cikin walwala ba tare da Wata tuhuma ba.