Mutane uku sun Jikkata sakamakon gobara a shagon siyar da Gas a Hotoro

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Al’ummar Layin Garsan Fulani cikin Unguwar Hotoron Arewa a Karamar hukumar Nasarawa da ke nan Kano sun shiga cikin dimuwa sakamakon tashin Gora a shagon siyar da Gas.

Wani da abin ya faru a idon sa Malam Abdullahi ya bayyana wa manema labarai cewa wutar ta tashi ne sakamakon kan tukunyar gas ya da ki keken dinki.

Lamarin ya shigar da mautanen yankin cikin tsoro Wanda hakan ya sa makotan shagon guduwa daga gidajen su domin neman mafaka.

Wani shaidar gani da ido ya ce mutane uku sun sami raunuka ciki harda wata matar Aure dake makwabtaka da shagon, yayin da wutar ta tarwatsa masu kade-kaden bukukuwan aure a kusa da abin da ya faru.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Saminu Yusif Abdullahi ya ce sun sami Kira daga wani Malam Anas Musa da misalin karfe 8:52 cewa wani shagon siyar da Gas ya kama da wuta a Hotoro tsamiyar Boka layin Garsan Fulani.

Kadaura24 ta rawaito cewa Saminu Yusuf ya ce suna samun lamarin suka yi gaggawar tura jami’an su inda cikin kankanin lokaci suka shawo kan matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...