Yanzu-Yanzu : IG ya dakatar da Abba Kyari kan zargin Rashawar miliyoyin daloli na Hushpuppi

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nigeria Usman Alkali Baba, ya amince da dakatar da DCP Abba Kyari daga Rundunar ‘Yan sandan Najeriya har zuwa lokacin da sakamakon binciken da ake Yi akansa Zai kammala.

Kadaura24 ta rawaito Cikin Wata wasika mai dauke da kwanan wata 31 ga Yuli, 2021, ya amince da shawarar dakatar da jami’in, Inda yace hakan ya yi daidai da matakan ladabtarwa na rundunar.

Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Frank Mba ya fitar a safiyar Ranar Lahadi nan yace IGP ya kara da cewa dakatarwar ana kuma sa ran zata samar da yanayi mai kyau ga kwamitin bincike na musamman na Rundunar don gudanar da bincike kan manyan zarge -zargen da ake yiwa DCP Abba Kyari ba tare da tsangwama ba.

Kwamitin Binciken na Musamman (SIP), wanda ya kunshi Manyan Jami’an ‘Yan Sanda guda hudu (4), yana karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, Mataimakin Babban Sufeto Janar na‘ yan sandan da ke kula da sashin binciken manyan laifuka (FCID). Hukumar ta SIP, Kwamitin Binciken zai gudanar da cikakken nazari kan dukkan zarge -zargen da gwamnatin Amurka ke yiwa DCP Abba Kyari kamar yadda yake kunshe cikin takardun da suka dace da hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya (FBI).

Sanarwar tace Kwamitin din kuma zai sami cikakken wakilcin DCP Abba Kyari ga dukkan zarge -zargen da ake yi masa, da gudanar da bincike kamar yadda ya dace, da kuma gabatar da shawarwari don jagorantar karin ayyukan da Jagorancin Rundunar a kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...