Ruwan Sama ya jefa makabartar Rimin kebe cikin mummunan hali

Date:


Daga Ibrahim Aminu Rimin kebe.

Makabartar unguwar Rimin kebe dake yankin karamar hukumar Ungogo tana Cikin Wani mummunan hali Sakamakon yadda ake Samun ruftawar kaburbura,

Wanda wannan alamarin ya faru ne a sakamakon ruwan da aka samu a daran Ranar Juma’ar data gabataj, lamarin ya sanya tarin kaburbura masu yawan gaske suka rufta.

Al’ummar yankin sun shaidawa Kadaura24 cewa sun rubuta takardar Neman daukin mahukun karamar hukumar ta Ungogo amma Kuma shiru kaji, Wanda a cewar shugaban kwaminitin makabartar unguwar Riminkebe Alhaji Muhammad Sani hattama shugaban kwaminitin makabartar na jihar wato Malam Ado Kurawa yasan da wannan matsalar ta ruftawar kaburbura a makabartar a unguwar ta Riminkebe.

Lamarin dai a cewar Alhaji Sani ya zuwa yanzu babu abunda suke Bukata face kasar da zasu cike kaburburan da suke a bude a yanzu haka, ya Kara da cewar ya zuwa yanzu basu tantance adadin kaburburan da suke a bude ba.

Ya cewa a yanzu haka kasar data rage musu bata fi mangala uku ba, ba rantama har su shiga aikin rufe kaburburan.

Daga karshe shugaban kwaminitin makabartar unguwar Riminkebe Alhaji Sani Muhammad yayi kira ga gwamnati a kowa ne mataki da kuma daidaikun al’umma Musamman mawadata dasu kaiwa makabartar dauki, ko Babu komai ita makarantar gidan kowa ce.

95 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...