Daga Surayya Abdullah Tukuntawa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa kan kisan kiyashin da ake yi wa ‘yan kasar nan, ciki har da shugaban ‘yan sintiri da kuma shugaban Dabna, a kauyen Dugwaba da ke karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa.
Shugaban yana mayar da martani ne kan abin da ya faru a ranar Laraba, yana cewa, “Yadda ake nuna rashin imani da rashin tausayi ba za mu bari duk mai hannu ya tafi haka ba, duk wani mai laifi sai mun hukunta shi”.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban, Garba Shehu ya fitar shugaban ya bai wa jami’an tsaro umarnin “Su ninka kokarinsu da kuma matakan da suke dauka kan wadannan bata gari cikin gaggawa”.
Buhari ya kuma umarci ma’aikatar ba da agaji da ta duba abin da aka yi asara a yankin a kuma aika musu da taimakon gaggawa.