Ranar Damokaradiyya: Ganduje yace Zai yi Magani Yan takarar da Suka sa aka Daga Fastar sa

Date:

Daga Abubakar Sa’eed

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi Yan Siyasa da Yan takara da su guji sa a Daga Hotunan su a taron Ranar Damokaradiyya ta bana da za’a gudanar Ranar Asabar.

Ganduje ya bayyana hakan ne Yayin Bikin baiwa Matasa da Dalibai Motoci domin bunkasa harkokin su.

Ganduje yace ba zai lamunci Yan Siyasa su Rika sawa ana Daga Hotunan su a Yayin taron Ranar Damokaradiyya ba Saboda akwai Manyan Baki da zasu Shigo jihar nan.

“Duk Dan takarar da ya baiwa Matasa Kayan maye ko Makami suka shiga dasu wajen taron mu to da kaina Zan sa a Kama yaron, Sannan Kuma Zan yi Maganin Wanda ya basu”. Inji Ganduje

Yace Shugaban jam’iyyar APC na Kasa da sauran Shugabanin jam’iyyar Za su halarci wajen taron na Ranar Damokaradiyya ta bana.

Gwamna Ganduje yace bayan Sunan Shugaban Kasa Muhd Buhari da Sunan Shugaban jam’iyyar APC na Kasa dana Gwamna Kano bama so muji an kirawo Sunan Wani Dantakara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan ganin wata Zulhijja, Saudiyya ta sanar da Ranar Arfat

Hukumomi a kasar saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin...

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano

Babbar Kotun Shari’a da ke Kano ta yanke hukuncin...

Sarkin Musulmi ya umarci yan Nigeria su fara duban watan Zulhijja

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar...

Yadda Rikici ya barke tsakanin yansanda da mutanen gari a Kano

Rahotanni daga Karama hukumar Rano dake jihar Kano a...