Fitaccen dan jam’iyyar APC da ke jihar Kano a arewacin Najeriya Alhaji Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya shaida wa BBC cewa sun kafa abin da suka kira ‘APC Akida’ ne domin dawo da martabar jam’iyyar a jihar ta Kano.
Dan Bilki Commander, wanda na hannun-daman shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne da suka dade suna gwagwarmayar siyasa tare, ya kara da cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ba ta kishin talakawa shi ya sa suka balle suka kafa ‘APC Akida’ domin wayar da kan jama’a kan irin illolin da take yi wa talakawa.
Ya kara da cewa nan gaba kadan za su fito da cikakkun bayanai kan yadda za su kwace ikon dukkan APC daga hannun magoya bayan gwamnatin jihar.
A cewarsa: “Gwamnatin jihar Kano ba ta kishin talakawa don haka muke ganin bai kamata mu ci gaba da tafiya tare da ita ba. mu ne muka kafa jam’iyyar APC kuma mun lura cewa ba sa bin ka’idoji da jam’iyyar ta shimfida shi ya sa muka balle daga cikinsu.”
Ya musanta zargin da ke cewa sun kafa APC Akida ne saboda korar da jam’iyyar ta APC ta yi musu, yana mai cewa “ai mu babu wanda ya isa ya kore mu daga wannan jam’iyyar domin da mu aka yanke mata cibiya