Daga Surayya Abdullah Tukuntawa
01-06-2021
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta rufe wasu gidaje biyu a Kano da ake zargin mallakar Birgediya-Janar Jafaru Mohammed, daraktan kudi da gudanarwa a ofishin mai ba da shawara ga Shugaban Kasa kan harkokin tsaro, Babagana Monguno.
Tun da aka fara binciken, majiyoyi sun ce Mungunu ya na amfani da ofishin sa, inda ya ke ta kokarin hautsina binciken saboda tsoron kada kadarorin biliyoyin nairori su zamo suna da alaka da shi.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, sojoji da ake zargi bisa ga umarnin NSA sun yi barazanar harbe jami’an hukumar EFCC da suka zo don nuna kadarorin da aka karba daga hannun Mohammed a rukunin gidajen Sun City, Lokogoma, Abuja
Ba tare da matsin lambar NSA da dakatar da binciken ba, jami’an hukumar hana almundahana a ranar Litinin sun isa wasu gidaje guda biyu, wadanda ke kan titin Gidado, kusa da titin Ahmadu Bello Way, Kano kuma an sanya musu alamar “EFCC” a kan gine-ginen.
Har ila yau, jami’an sun sanya alama kan wata kadara mallakar wakilin na NSA a Hotoro GRA, Kano.
Majiyar DAILY NIGERIAN ta bayyana cewa EFCC ta sanya alama a kalla kadarori goma da ke da nasaba da hafsan sojan da ke aiki a Kano ranar Litinin.
Mai shari’a Folashade Ogunbanjo a karar da ke da lamba FHC / ABJ / CS / 007/2021 ta bayar da umarnin a kwace wasu kadarori takwas da ke da alaka da Mohammed wanda amintaccen mataimaki ne ga NSA, Manjo Janar Babagana Moguno (mai ritaya).