Ummi Zeezee Ta Gana Da Kwamishinar Mata Ta Kano Kan Yunkurin Kashe Kanta

Date:

Daga Abubakar Sa’eed Suleman

Fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood a Najeriya Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta gana da Kwamishinar mata ta Kano Zahra’u Muhammad bayan da jami’ar gwamnatin ta nemi ta ganta kamar yadda Ummi ta fada.

Ganawar ta su na zuwa ne, bayan da a farkon watan Afrilu, Ummi ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, tana ji kamar ta kashe kanta.

Ba a san takamaiman lokacin da suka gana ba, amma a karshen makon da ya gabata Ummin ta wallafa hotunta tare da kwamishinar.

“Malama Zahra’u na je mun zauna ta min nasiha ne sosai mai ratsa jiki, da na ce zan kashe kaina.” Ummi ta rubuta a shafinta na Instagram.

“Don haka, ina godiya ta musamman zuwa ga kwamishina Zahra’u, dangane da yadda ta nuna damuwarta har ta ce in zo ta ji  matsalar da ta sa nake so na kashe kaina.”

Ummi ta kuma nuna takaicinta kan yadda mutane da dama suka yi ta “zaginta” a lokacin da al’amarin ya faru, tana mai cewa kamata ya yi, a yi mata nasiha ba ci mata mutunci ba.

Ta kara da cewa, “ban san lokacin da na fashe da kuka ba, domin ni na dade ban ga mace mai imani da sanin darajar rayuwar dan adam ba.”

Jarumar dai ta yi ikrarin cewa wani abokin harkarta ne dan kabilar Igbo ya damfare ta naira miliyan 450 a wata harkar mai da suka kulla.

Hakan ta ce ya sa, ta fara tunanin kashe kanta, saboda kuncin rayuwa da ta shiga sanadiyyar wannan damfara.

Wannan batu ya janyo ce-ce-ku-ce a Kannywood da kuma daga masu bibiyar fina-finan masana’antar wacce ke arewacin Najeriya.

Bayan kwanciyar kurar wannan lamari, Ummi ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, ta ji labarin kwamishinar na so ta ganta, abin da ya kai ga wannan haduwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...