Goman Karshe: Sakon A B Kaura ga al’ummar Musulmi

Date:

Daga Abdulrazak Bello Kaura

BARKA DA SHAN RUWA
Da yake yau an kai azumi 20 an shiga Daren 21 DAREN DA AKE FARA TUHAJJUD a wasu Masallatai

Bayan addu’ar Neman gafara da aminci a duniya da lahira da addu’ar samun zaman lafiya da tsaro ga jihar mu da kasa baki daya da sauran addu’o’in da za mu yi.

Yana da kyau mu roki Allah DUK MAI HANNU WAJEN GALLAZAMA AL’UMMAR KAURAN NAMODA DA KEWAYE AKAN WUTAR LANTARKI ALLAH YA MANA MAGANIN SHI KO WAYE SHI KO KUMA KO SUWAYE SU.

Lamurran kasuwanci da na jin dadin al’umma da yawa sun ta’allaka akan wutar lantar ki, amma mun rasa dalilin da kesa ana gallaza mana. Kaga wuta tun da Gusau har last garin da ke kusa da Kaura amma cikin garin Kaura Babu ita.

Har wani wurin kashe wuta aka yi a bakin Barikin Sojoji dake Tashar Rawayya, a kashe mana wuta amma su a basu, don ana tsoron su, masu kunno wutar (TCN) sun San sun ba layin Kaura amma a kan hanya an hana wutar isowa Kaura.

Don Allah kowa ya taimaka da addu’a a cikin sujada da sauran lokuta Allah ya kwatar mana hakkin mu, Allah ya Isar ma al’ummar Kaura Namoda ga duk mai hannu a cikin wannan lamari musamman idan da gangan ake yi mana

Gomnati taki cewa komi, an bar mu muna rigima da mutane marasa tausayin al’umma yan KAEDCO suna zaluntar bayin Allah saboda wani tunani nasu na daban.

Allah ka amintar da mu kasa mu dace da Daren LAILATUL QADRI ka biya mana da duka bukatun mu ka sada mu da alkhairi marar yankewa ka taimaki masu taimakon bayin ka musamman marayu da mabukata.

A.B.Kaura
Development Journalist

Arewa Agenda

#prnigeria

112 COMMENTS

  1. Українець Олександр Усик (18-0, 13 КО) зможе нокаутувати британського чемпіона Ентоні Джошуа (24-1,22 КО). При цьому для нашого співвітчизника не стане проблемою перевагу суперника в габаритах Усик Джошуа дивитися онлайн Усик Джошуа – Девід Хей поставив хрест на українця

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...