Hukumar DSS ta gargadi Malaman addini kan kalaman su

Date:

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) ta bayyana cewa daga yanzu ba za ta kawar da kai daga wasu mutane da ke neman tayar da zaune tsaye a kasar ba.

DSS ta soki abin da ta kira wasu kalamai na marasa son zaman lafiya da ke barazana ga gwamnati da dorewar kasar.

Ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi.

“Abin da ya ja hankalinmu shi ne kalaman da ba su dace da kuma wasu ayyukan malaman addini da shugabannin siyasa da suka gabata wadanda ko dai suka yi kira a cire gwamnati da karfi ko mkuma suke so a yi tarzoma. Mu gano cewa sun yi hakan ne domin kawo rashin zaman lafiya,” a cewar DSS.

Hukumar ta kara da cewa abin takaici ne mutanen da ake gani da kima suna yin irin wadannan kalamai domin biyan bukatun kashin kansu.

“Muna masu tuna musu cewa kodayake mulkin dimokradiyya ya bayar da ‘yancin fadar albarkacin baki, amma ba ta bayar da damar yin kalamai na ganganci da ka iya shafar tsaron kasa ba,” in ji hukumar ta DSS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kwamitin PTA na Kano ya dauki matakan hana ragewa dalibai hanya bayan taso su daga makaranta

DAGA ABDULHAMID ISAH Shugaban Kwamitin Iyayen yara da Malamai na...

Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad

Daga Zainab Nasir Ahmad Mai Girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Abba...

RATTAWU ta Kano ta taya Abbas Ibrahim Murnar sabon mukamin da NUJ ta ba shi

Kungiyar ma'aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar...

NUJ ta kasa ta baiwa Abbas Ibrahim sabon mukami

Daga Aliyu Abdullahi Danbala   Kungiyar yan Jarida ta Nigeria ta...