Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa
Gwamnatin jihar Bauchi ta haramtawa Sheikh Abubakar Idris, wa’azi da jagorantar Sallah a jihar ta Bauchi.
A cikin wata kwafin takarda da Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Bauchi. Hon Ahmad Aliyu Jalam. Ya ce an hana malamin yin wa’azi da Limanci a duk fadin Jihar Bauchi Dangane da yadda malamin ya gabatar da hudubarsa, yana zagin Sahabban Manzon Allah (S A W )wanda hakan na iya haifar da sabani tsakanin al’ummar Musulmi dake jihar ta Bauchi.”
Sheikh Abubakar Idris na Asasu shi ne shugaban makarantar Asasudeen da ke Azare wacce ke da dimbin magoya baya Yana wa’azi a unguwar Azare.
Malam Abubakar Idris ya kasance yana kwaikwayon salon wa’azin Shekh Abduljabbar kabara wanda ya ce akwai Hadisai na jabu da wasu Sahabbai suka ruwaito hadisan karya a cikin littattafan Musulunci. A sakamakon haka, an samu rashin jituwa da rashin fahimta tsakanin malamai da Abduljabbar Kabara da wasu malamai a jihar ta Kano.
Mal Abubakar Asasu ya kuma yi kokarin tattaunawa da wasu malamai kan fahimtarsa kafin Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki wannan matakin akansa.
wasu wakilin Manema labarai a Azare sun yi kokarin tuntubar malamin don jin matsayarsa kan matakin da aka dauka a kansa. Amma har zuwa yanzu ba su hadu da shi ba , da zarar sun samu damar ganin sa kuma za mu yi hira da shi don jin ta bakin sa.