Zagin Sahabbai :Gwamnatin Jihar Bauchi ta Haramtawa Wani Malami Wa’azi Da Jagorantar Sallah a Bauchi

Date:

Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa

 Gwamnatin jihar Bauchi ta haramtawa Sheikh Abubakar Idris, wa’azi da jagorantar Sallah a jihar ta Bauchi.
 A cikin wata kwafin takarda da Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Bauchi. Hon Ahmad Aliyu Jalam.  Ya ce an hana malamin yin wa’azi da Limanci a duk fadin Jihar Bauchi Dangane da yadda malamin ya gabatar da hudubarsa, yana zagin Sahabban Manzon Allah (S A W )wanda hakan na iya haifar da sabani tsakanin al’ummar Musulmi dake jihar ta Bauchi.”  
Sheikh Abubakar Idris na Asasu shi ne shugaban makarantar Asasudeen da ke Azare wacce ke da dimbin magoya baya  Yana wa’azi a unguwar Azare.


Malam Abubakar Idris  ya kasance yana kwaikwayon salon wa’azin Shekh Abduljabbar kabara wanda ya ce akwai Hadisai na jabu da wasu Sahabbai suka ruwaito hadisan karya a cikin littattafan Musulunci. A sakamakon haka, an samu rashin jituwa da rashin fahimta tsakanin malamai da Abduljabbar Kabara da wasu malamai a jihar ta Kano.  


Mal Abubakar Asasu ya kuma yi kokarin tattaunawa da wasu malamai kan fahimtarsa ​​kafin Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki wannan matakin akansa.  


wasu wakilin Manema labarai a Azare sun yi kokarin tuntubar malamin don jin matsayarsa kan matakin da aka dauka a kansa.  Amma har zuwa yanzu ba su hadu da shi ba , da zarar sun samu damar ganin sa kuma za mu yi hira da shi don jin ta bakin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...