Cin hanci ba zai bar Najeriya ta ci gaba ba – Ganduje

Date:

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ba za ta taba ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta.

Ganduje ya ce babu yadda za a yi kasar nan ta ci gaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a Najeriya.

“Za ku yarda da ci idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba,” in ji Ganduje.

Ganduje ya bayyana hakan ne ya yin kaddamar da wani kwamitin na mutum takwas kan wasu dabarun yaki da rashawa a jihar.

An kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis da nufin rage cin hanci da kuma tabbatar da an gudanar da al’amura a bude a fadin jihar, in ji Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji.

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...