A Nigeria Mutane 239 Yan Bindiga suka kashe a wata guda – Bincike

Date:

A cikin mako guda, an kasha mutane akalla 239 a Najeriya da suka hada da jami’an tsaro, sannan aka yi garkuwa da 44, lamarin da ke dada fito da matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

An yi kisan ne a sassan kasar da suka hada da babban birnin tarayya Abuja da ke zama fadar gwamnatin Nigeria.

Alkaluman da aka tattara sun nuna cewa, an kashe mutane 20 a ranar Lahadi ta makon Daya gabata, 5 a ranar Litinin, sai 6 a ranar Talata, inda aka kashe 85 a ranar Laraba a Karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Shafin Radio Farance ya rawaito cewa an salwantar da rayukan mutane 60 a kauyen Magami a ranar Juma’ar da ta gabata.

Haka ma wasu dalibai 3 na Jami’ar Greenfiled mai zaman kanta a jihar Kaduna sun rasa rayukansu bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su, yayin da wasu jami’an ‘yan sanda a jihar Anambra su ma suka mutu a wani farmaki da aka kaddamar kan shalkwatansu.

Hare-hare a sassan Najeriya sun tsananta, inda ‘yan bindiga ke far wa kauyuka da kasuwanni da wuraren ibada har ma da matafiya da ke bin babbar hanya.

77 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...