December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Yanzu-Yanzu : Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Ungoggo Ya Rasu

Daga Jamili Dantsoho Bachirawa

A safiyar Lititin din ne aka sanar da Rasuwar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Ungoggo Hon. Abdullahi Dantalata Karo .

Shugaban Karamar Hukumar Ungoggo Engr Abdullahi Garba Ramat ne ya sanar da Rasuwar Mataimakin nasa a sahihin shafinsa na Facebook.

“Innalillahi wa inna’ilaihirraj’un Allah kaji kan Abdullahi Dantalata Karo ( Vice chairma Ungogo LGA), Ka yafe masa kura-kuren sa, Ka bawa iyalansa hakuri da dangana, intamu tazo kasa mucika da imani.
Hasbunallah wani’il wakil.😰” Inji Engr. Ramat

Kafin Rasuwar Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Ungoggon ya taba Zama shugaban jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Ungoggo daga bisa bayan ya fito takarar Shugabancin Karamar Hukumar Kuma Allah ya bashi Mataimaki.