Annubar Kwalara: Sarkin Bichi ya Kai tallafin Magunguna Asibiti

Date:

Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Dr. Nasir Ado Bayero, ya Siyo Magunguna Kyauta Domin Mikawa ga Babban Asibitin Dake Garin Bichi Don taimakawa Masu Amai da Gudawa a Yammancin Yau Laraba.

Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Dr. Nasir Ado Bayero, yabada Mika kayane ta hannu Mai Girma Hakimin Bichi Dandarman Bichi Alh. Abdulhamid Ado Bayaro.

Dayake Karbar kayan Shugaban karamar Hukumar Bichi Dr.Yusif Muhammad Sabo,Wanda Yasamu Wakilcin Kansilan Lafiya Hon. Haruna Sani Ahmad ya godewa Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Dr. Nasir Ado Bayero bisa Wannan abun alkhairi daya Kai Asibitin .

Sarkin ya nuna alhininsa bisa Wannan iftila’in na Amai da gudawa da ya addabi al’umma a yankin Masarautar tasa.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Sarkin Bichin ya jajantawa al’ummar Sannan yayi musu fatan samun Sauki har ma a bukaci al’ummar Masarautar dasu Mai da hankali wajen bin shawarwarin likitoci domin gujewa kamuwa da Annubar.

78 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...