Daga Fa’iza Bala Koki
Mai martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero ya hori sabon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai kula da jihohin Kano da jigawa Ede Ayuba ekpeji da ya kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi sabon AIG wanda ya kasance a fadar domin gabatar da kansa tare da neman goyon baya da hadin kai.
Sarkin ya kuma shawarce shi da ya kasance mai gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa tare da bada tabbacin majalisar masarautar kano na bada goyon bayan don inganta harkokin tsaro a jihar kano.

Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24 yace tun da farko sabon AIG Mista Ede ya jaddada kudirinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kuma tabbatar wa Sarkin cewa zai yi bakin kokarinsa wajen ganin an kawar da matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma musamman a lokacin zabe mai zuwa tare da neman goyon bayan sarkin ta wannan hanyar.
A wani labarin kuma mai martaba Sarkin Bayero ya karbi bakuncin ma’aikatan babban bankin Najeriya, Inda ya bukaci su dasu dage da wajen wayar da kan al’umma muhimmancin te-Naira da batun canjin kudin da gwamnatin tarayya za ta yi nan ba da dadewa ba.
Daraktan kudi Alhaji Ahmad Bello umar, ya shaida wa Sarkin cewa sun je fadar ne domin neman goyon bayan sarkin akan aiyukan banki.